By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da nadin tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Babatunde Olaniyan, a matsayin shugaban kungiyar wasanni ta Shooting Stars wanda aka fi sani da 3SC.
Makinde ya sanar da nadin ne a ranar Juma’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa idan za a tunawa Olaniyan ya wakilci mazabar Ibadan ta Arewa ta 1 a majalisar dokokin jihar Oyo a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, inda ya zama mataimakin kakakin majalisar.
Ya lashe zaben ne a karkashin jam’iyyar AP.
Makinde, a cikin wasikar nadin da sakataren gwamnatin jihar, Olubamiwo Adeosun, ya sanya wa hannu a madadinsa, ya bukaci sabon shugaban hukumar da ya yi aikinsa tare da “cikakkiyar biyayya”.
Ya ce, “Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Gwamnan Jihar Oyo, ‘Seyi Makinde, ya amince da nadin ku a matsayin shugaban kungiyar wasanni ta Shooting Stars (3SC) daga ranar 24 ga watan Fabrairu, 2022.
Olaniyan ya yi digiri na farko a fannin Kinetics da Ilimin Lafiya a Jami’ar Ibadan.
Sannan ya yi aiki a matsayin shugaban makarantar horas da alkalan wasan kwallon kafa ta jihar Oyo tun a shekarar 2004 sannan kuma ya taba rike mukamin kwamishinan wasannin gasar Premier tun shekarar 2010.