Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki daliban makarantar Ojodu Grammar School da suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya faru a ranar Talata a hanyar Isheri, dake yankin Ojodu na jihar Legas.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Larabar ta hannun Femi Adesina, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Buhari ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Legas da kuma mahukuntan makarantar Ojodu Grammar School kan bakin ciki da raɗaɗin rashin rayuka da aka yi sanadiyar Hadarin Motar da ya afku a jiya Talata
Shugaban na Najeriya ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka Mutu sanadiyar Hadarin Motar, ya kuma baiwa wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito a ranar Talata cewa wata Babbar mota ta Murkushe Daliban wata makaranta a unguwar Ojodu-Berger da ke Legas Yayin da suke kokarin tsallake hanya zasu koma gidajensu.
Lamarin wanda ya afku a tashar mota ta Grammar a ranar Talata da rana ya haifar da zanga-zanga yayin da daliban makarantar Babs Fafunwa Millennium da wasu Yan daban, suka far wa ‘yan sanda da duwatsu tare da lalata wasu motoci.
An kai mutane da dama da suka jikkata sakamakon hatsarin zuwa asibitoci daban-daban dake jihar, yayin da aka kama direban motar.