Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu a matsayin Manajan Daraktan Hukumar buga kudi da muhimman takardu NSPMC Plc.
An ce Halilu yaya ne ga uwargidan shugaban kasa, A’isha Buhari, kuma ya jagoranci hukumar ne a matsayin riko bayan murabus din Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku ceto Ƴan Najeriya daga Ƴan Ta’adda – Ortom ga Fadar Shugaban Ƙasa
Rahotanni sun ce shugaban ya amince da nadin ne biyo bayan shawarar da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayar, wanda ke rike da mukamin shugaban hukumar NSPMC.
Halilu ya halarci babban kwas na 39, a shekarar 2017 na National Institute for Policy and Strategic Studies Kuru dake Jos, wanda ya kai ga samun lambar yabo ta Memba na Cibiyar National Institute, mni.
Ya yi digirin farko a fannin Noma B. Masters in Business Administration, da Masters in International Affairs and Diplomacy, duk a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Har ila yau, ya bayyana cewa yana da gogewar sama da shekaru 23 a harkar banki, inda ya yi aiki da bankin kasa da kasa na African International Bank Limited, AIB, da Zenith Bank Plc, kuma mamba ne a Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya, NIM.
A wani labarin kuma, Yadda zan haɗa kan Najeriya idan aka zabe ni – Peter Obi
Dan Takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi ya yi nuni da yadda gwamnatinsa za ta hada kan Najeriya idan aka zabe shi a 2023.
Obi ya ce gwamnatinsa za ta yi kokarin sake hade Najeriya ta hanyar amfani da tanade-tanaden doka.