Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rubutawa majalisar dattawa wasika ta tabbatar da Anthony Ojukwu, domin sake nada shi a matsayin babban sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa.
A cewar wasikar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, sake nadin na shekara biyar ne kuma zai kasance wa’adin karshe na Ojuku a kan mukamin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Jami’an DSS Sun Cafke Alhassan Ado Doguwa A Filin Jirgin Sama
Wasikar ta ce, “A bisa tanadin sashe na 7(2) na dokar hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa, na shekarar 2010, na rubuta wasika zuwa ga majalisar dattawa domin ta tabbatar da nadin Mista Anthony Ojukwu, SAN.domin sake nada shi a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa, na wa’adin karshe na shekaru 5.
“Yayin da nake fata Majalisar Dattawa za ta yi nazari tare da tabbatar da nadin kamar yadda aka saba a cikin gaggawa. Da fatan za a amince da irin tabbacin da Shugaban Majalisar Dattawan ya ba ni mafi girman la’akari da ni.”
Haka kuma, a wata wasika mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Fabrairu, 2023, shugaban ya kuma nemi a tabbatar da nadin Hon. Mai shari’a Stanley Lawal, a matsayin shugaban kotun daukaka kara ta Kwastomari dake Abuja.
Tabbatar da hakan, a cewar shugaban, ya yi daidai da sashe na 266(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Wasikar ta ce, “Na ji dadin mikawa majalisar dattawa domin tabbatar da nadin Hon. Mai shari’a Stanley, Adekunle Lawal, mukaddashin shugaban kotun daukaka kara na babban birnin tarayya Abuja, a matsayin shugaban kotun.
“Na yi imanin cewa Majalisar Dattawa za ta yi nazari tare da tabbatar da wanda aka nada ta hanyar da ta saba. Da fatan za a yarda, mai girma shugaban majalisar dattawa, tabbacin mafi girma na.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Tinubu ya doke Peter Obi da Atiku a Rivers
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, ya lashe zaben da aka gudanar a jihar Rivers.
Dan takarar jam’iyyar APC ya kuma lashe jihohin Neja da Benue, inda ya samu kuri’u masu tarin yawa a jihohin biyu.