Jam’iyyar PDP a yankin Borno ta tsakiya ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a baya bayan nan saboda kura-kuran zabe da kuma kin shigar da sakamakon zabe daga rumfunan zabe zuwa BVAS da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC tayi bisa ka’idojin Dokar Zabe na 2022,Vanguard ta rawaito.
An bayyana hakan ne a ranar Talata a cibiyar NUJ da ke Maiduguri yayin wata sanarwar hadin gwiwa da dan takarar kujerar Sanatan Borno ta tsakiya na jam’iyyar PDP Barista Umara Kumalia da wasu ‘yan takarar majalisar wakilai daga kananan hukumomi takwas da ke shiyyar suka sanya wa hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Sake Nada Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta Kasa
Kumalia wanda ya karanta sanarwar yana tare da Babakura Abba, dan takarar majalisar wakilai ta tarayya Maiduguri, Ahmad Mohammed Zannah, Dan Takarar Majalisar Wakilai ta tarayya, Dikwa, Mafa, Konduga da Abdulrazaq Ahmed Zanna, Dan Takarar Majalisar Wakilai Bama, Gamborin Ngala, Mazabar tarayya ta Kala Balge, sai Muhammad Abdallah, Dan Takarar Majalisar Wakilai Jere na tarayya.
‘Yan takarar sun bayar da misali da yadda suka yi zargin cewa adadin wadanda aka amince da su masu rijista a karamar hukumar Bama ya kai kusan 18,000 yayin da adadin kuri’un da aka kada ya kai 21,850. Koyaya, an ƙaddamar da adadi na 22,076 sama da 18,000 a matsayin jimlar adadin waɗanda aka amince da su masu rijista.
Ya ku ‘yan jarida kamar yadda kuka sani, an gudanar da zabukan kananan hukumomi takwas da ke yankin Borno ta tsakiya ba tare da bin ka’idojin tsarin zabe ba kamar yadda kundin tsarin zabe da dokar zabe ta 2023 ta bayyana.
“Kananan hukumomi takwas da ke Borno ta tsakiya sune Maiduguri Metropolitan, Jere, Konduga, Bama, Mafa, Dikwa, Gamboru Ngala da Kala Balge.
“Magudin ya shafi zaben shugaban kasa, da majalisar dattawa da na wakilai.
“A dukkan kananan hukumomi takwas, an yi watsi da amfani da na’urar BVAS saboda an ba mutane takardun dongwala kuri’a hannu da hannu ba tare da amfani da na’urar BVAS ba. An yi ta samun yawaitar kada kuri’a a fadin kananan hukumomi takwas, da sauya takardar sakamakon zaben bayan kammala zaben da dai sauransu.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Jami’an DSS Sun Kama Alhassan Ado Doguwa A Filin Jirgin Sama
Jami’an Rundunar ‘yan sandan tsaron farin kaya sun kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane tare da kona sakatariyar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a yayin zaben da aka kammala.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa akalla mutane uku ne suka mutu a lokacin da aka kona sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada.