Babban mataimaki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Garba Shehu ya bayyana adadin ayyukan yi da gwamnati mai ci ke samarwa a fannin noma abin a yaba ne.
A cewar Shehu, gwamnatin Buhari ta yi nasarar samar da sabbin guraben ayyukan yi miliyan 12 a fannin noma kadai.
KU KARANTA: FG Ta Jaddada Kudurinta Na Kakkaɓe Cutar Daji A Najeriya
Wannan bayanin ya fito ne a wata tattaunawa ta musamman da Shehun a gidan Talabijin na Channels.
Shehu ya bayyana irin ayyukan da gwamnatin ke yi a sassa daban-daban da suka hada da tsaro, wutar lantarki, da yaki da cin hanci da rashawa.
Shehu ya kara da bayyana irin gagarumin ci gaba da aka samu a harkar noma, inda ya ce, A fannin noma kadai, kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN) shaida ce kan batun samar da sabbin ayyukan yi miliyan 12.
Ya ci gaba da bayyana yadda wannan gagarumin karuwar noman taki ya yi tasiri ga manoman shinkafar kasar nan, wanda ya haifar da karuwar noman shinkafa a cikin gida.
Hakan ya sa Najeriya ta samu wadatar abinci tare da habaka tattalin arzikinta, inda ta fice daga dogaro da bangaren Ababan da akan shigo da su nan Najeriya.
Ya kara da cewa duk wannan nasarori an same su ne, bisa kulawar shugaba Buhari wanda a kullum bashi da wani buri illa taimakon manoma.
A wani labarin kuma: Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi
Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi