Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na inganta harkokin kiwon lafiya ga masu fama da cutar daji.
Cibiyar Nazarin Ciwon dajin ta Kasa (NICRAT), ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a Abuja.
KU KARANTA: Bashin $800m Da Buhari Zai Ciyo Ya Sabawa Kundin Tsarin Mulki — Sanatan Arewa
Bashin $800m Da Buhari Zai Ciyo Ya Sabawa Kundin Tsarin Mulki — Sanatan Arewa
Ya ce gwamnati na yin kokari tare don tabbatar da cewa masu fama da cutar daji sun sami ingantacciyar kulawa da kulawa da cutar.
Aliyu ya ce gwamnati ta sayo kayan aikin magance cutar a wuraren kula da ita.
A cewar sa, ba a samun irin wannan kokarin na inganta kula da cutar kansa a mafi yawan cibiyoyin kula da cutar kansa a baya musamman a cikin shekaru goma da suka gabata.
Ya ce ana kokarin samar da karin kayan aikin cutar a duk cibiyoyin cutar kansa guda bakwai da ke fadin kasar nan wadanda suka hada da na’urar kara samar da karin kuzari.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da horar da kwararrun likitocin cutar kanjamau don cike gibin da ke akwai.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar kula da masu cutar dajin ta kasa (ARCON) Dr Nwamaka Lasebikan ya ce an shirya taron ne domin bayar da shawarwarin kula da masu fama da cutar daji ta hanyar magance kalubalen.
A wani labarin kuma:
Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi
Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi