Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taya gidan rediyon tarayya na Kaduna da aka fi sani da Rediyon Kaduna murnar cika shekaru 60 da kafuwa.
Buhari ya yabawa gidan rediyon kan rawar da ya taka wajen hada kan al’ummar Najeriya, da kuma tabbatar da zaman lafiya da amincewar juna a lokacin yakin basasar kasar da kuma bayan yakin basasar da aka yi a kasar.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanyawa hannu a ranar Litinin.
Shugaban a cikin sakon bidiyo, (da harshen Hausa), ga mahukuntan gidan rediyon, ya yabawa gidan rediyon kan shirye-shiryensa na ilimantarwa, fadakarwa da kuma nishadantarwa wadanda suka kara kayatar da masu sauraronta a fadin Najeriya da makwaftan kasashe.
Bayanin kasa karin haske ne game da cikakken bayanin sakon bidiyon:
“Sunana Muhammadu Buhari, Shugaban Tarayyar Najeriya.
“Duniya a lokaci guda ta shaida irin rawar da Rediyon Najeriya Kaduna ta taka wajen hada kan al’ummar Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya da amincewa da juna a lokacin yakin basasar kasar da bayan yakin basasa.
“Saboda wadannan da sauran gudunmawar da gwamnatin tarayya ta bayar, gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen samar da na’urorin watsa labarai na zamani ga gidan rediyon.
“Radiyon Najeriya Kaduna ya yi kaurin suna wajen shirye-shiryensa masu ilmantarwa da fadakarwa da kuma nishadantarwa.
“Tashar rediyo ce da ke da yawan masu saurare a duk fadin Najeriya da ma makwabtan kasashe saboda karfin yada shi.
“Bisa la’akari da kalubalen da ake fuskanta a harkar yada labarai, gwamnatin tarayya na kokarin sake mayar da gidajen rediyonta domin samun ingantacciyar hidima.
“Ina kira ga mahukuntan gidan rediyon Najeriya Kaduna da su kiyaye gadon gidan rediyon na hada kan al’umma da wayar da kan al’umma kan muhimman batutuwan da za su bunkasa ci gaban kasa.