Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya zababben shugaban kasar Kenya, William Ruto murnar nasarar da ya samu a babban zaben kasar da aka gudanar a makon daya gabata.
A cikin sakon taya murna da kakakinsa, Mista Femi Adesina, ya fitar ranar Litinin a Abuja, shugaban ya kuma yabawa al’ummar Kenya bisa yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sifeton Yan sanda Ya Karrama Wani Jami’i A Kano, Bayan Ƙin Karbar Cin Hanci
Ya ce hakan ya sake nuna cewa tsarin dimokuradiyya, dabi’u da ka’idoji su ne hanya mafi dacewa da jama’a za su zabi shugabanninsu da kuma dora su a kan su.
A cewarsa, Najeriya na mutunta Kenya a matsayin abokiyar kawance a yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Buhari ya kuma ce, kyakkyawan tsarin hadin gwiwa a kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar Tarayyar Afirka, Majalisar Dinkin Duniya da kasashe Rainon Ingila, zai taimaka wajen kulla alakar taimakon kai.
A yayin da yake tayar murna nasarar rantsar da shi da kuma wa’adin mulki, shugaban ya ce yana fatan kara yin aiki mai kyau da inganci a tsakanin kasashen biyu.
Ya kuma lura cewa, kasashen biyu sun yi mu’amala da muhimman abubuwa kamar inganta zaman lafiya da tsaro a nahiyar, da dimokuradiyya, da bunkasar tattalin arziki da ci gaban al’umma.
Shugaban na Najeriya ya jinjinawa shugaba Kenya bisa irin kimar da yake da ita da kuma jagoranci nagari ga al’ummar Kenya cikin shekaru tara da suka gabata.
Ya kuma yaba masa bisa manyan abubuwan da gwamnatinsa ta gada a fannin samar da ababen more rayuwa, ilimi, sauye-sauyen harkokin kiwon lafiya da yawon bude ido da kuma gagarumin tasiri da goyon baya kan harkokin tsaro a yankin.