Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ya mikawa Baturen yan sanda na Nassarawa, SP Daniel Itse Amah takardar shaidar karramawa bayan Namijin kokarin da yayi wajen nuna rashin son zuciya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, karrama jami’in na zuwa ne bayan da yaki karbar cin hancin dalar Amurka dubu dari biyu (USD 200,000).
Wasu da ake zargi da laifin fashi da makami ne suka bayar da Toshi yar bakin, don ganin an saki yan’uwansu.
A cikin wata wasika mai kunshe da yabon, SP Daniel, babban sifeton ya yaba da yadda ya nuna kwarewa da kai zuciya nesa, tare da jajircewa wajen kama Ali Zaki.
Binciken da jami’an ‘yan sanda a karkashin SP Daniel ya jagoranta ya kai ga cafke ‘yan fashi da makami a Kano.
Don haka, an mayar da batun wannan kara zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja bisa umarnin IGP domin yin bincike mai zurfi.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da kamun ya kuma ce, “Lauyan da sauran wadanda ake zargi da hannu a cikin lamarin na tambayoyin da zasu amsa kuma har yanzu muna kan batun.”