Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Mutane 70 A Jamhuriyyar Nijar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a garin Zaroumdareye, wani gari da ke kan iyaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Mali da ‘yan ta-da-kayar baya suka yi, ya na mai bayyana lamarin da cewa wani kira ne na ganin an hada karfi da karfe don magance ta’addanci.
Shugaba Buhari ya ce, “Na yi matukar kaduwa da kisan mutane da dama marasa laifi” da wadannan mugayen tsageru suka yi.
A cewar Shugaban, “Muna fuskantar babban ƙalubale na tsaro saboda yaƙin da ake yi da ƴan ta’adda a yankin Sahel kuma daukar matakan hadin kai ne kawai zai taimaka mana wajen fatattakar wadannan muggan makiya jama’a”.
Ya bayyana cewa “ta’addanci yanzu ya zama kamar wata muguwar cuta wacce ke iya yaduwa a kowane lokaci matukar ba a dauki mataki na bai daya ba.”
Shugaba Buhari ya ce “rashin zaman lafiya a wani yanki na Afirka na da tasiri ga tsaron wasu wasu ƙasashen.”