Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Sanannen Malamin Addinin Musulunci, kuma Limamin Jami’ar Bayero, Kano Dr Ahmad Muhammad Ibrahim.
Sanannen Malamin ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Magoya bayan APC sun shigar da ƙara a kotu, suna neman ta hana babban taron jam’iyar na ƙasa
Haka zalika, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a cikin saƙon ta’aziyyar wanda Mai Magana da Yawun sa Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewar Dr Ahmad ya kasance Fitaccen Malami ne Fagen Hadisin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.
Yace Ahmed zai cigaba da zama wanda za’a riƙa tunawa a Musulunci da ƙasa baki ɗaya, da kuma son shi na wayar wa Al’umma kai.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewar Marigayin ya rubuta littattafai da dama a rayuwar sa, daga cikin wanda ya yi shine fassara Muwatta Malik zuwa Hausa, inda aka wakilci Shugaban Ƙasa.
Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan sa, Al’ummar Jami’ar Bayero, da Ɗaliban sa, da Mabiyan sa a Kano dama Arewa maso Yamma.