Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce idan ba tare da goyon bayan jama’a ba ga rundunonin soji “masu aiki tukuru”, za a dauki lokaci mai tsawo a Najeriya wajen kawo karshen yaki da ta’addanci, ‘yan fashi da garkuwa da mutane.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin liyafar buda baki ga ‘yan kasuwa da shugabannin jam’iyyun siyasa.
Buhari ya kuma yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasar kasarnan da su shiga domin damawa tare da su a yunkurin gwamnatinsa na dakile rashin tsaro.
Shugaban wanda ya bukaci jam’iyyun siyasa da su ajiye zabe da bambance-bambancen da ke da alaka da zaben a gefe, ya bayyana rashin tsaro a matsayin ‘’abokin gaba’’ da ke zaluntar kasa.
“Dole ne mu kiyaye kasarmu don samun ci gaba mai maana da kuma dorewa.
“Ina fatan ganin irin wannan kudirin a alakar da ke tsakanin jam’iyyu da gwamnati, musamman ganin nan ba da jimawa ba kakar zabe ta zo mana,” inji shi.
Shugaban, yayin da yake magana kan saukin kasuwanci a kasar, ya shaidawa shugabannin masana’antu da shugabannin siyasa a wajen liyafar cin abincin cewa gwamnatinsa ta yi kokari matuka wajen inganta harkokin kasuwanci.
Ya bukaci kamfanoni masu zaman kansu da su kara kaimi ga kokarin gwamnati na rage radadin talauci da samar da ayyukan yi ga matasa.