Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Ogun ranar Alhamis domin kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Dapo Abiodun ya aiwatar a jihar.
Tun da farko dai, An dage ziyarar da Shugaba Buhari zai Kai jihar a jihar ne, a ranar 21 ga Disamban shekarar 2021.
Sai dai a yau Lahadi gwamnatin jihar ta yi nuni da cewa shugaban kasar ya Mai da ziyarar tasa ta kwana daya a ranar Alhamis 13 ga watan Janairu shekarar 2022.
A cewar sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Kunle Somorin, ya fitar, ya ce, gwamnatin jihar za ta tar bi Shugaba Buhari a filin ajiye motoci na Gateway City Monument Park da ke hanyar Sagamu, da karfe 10 na safe, inda shi ne zai kaddamar da aikiyukan da gwamnatin jihar ta yi.
Sanarwar ta kara da cewa, baya ga kofar shiga birnin, sauran ayyukan da ake sa ran shugaban zai kaddamar sun hada da babbar hanyar Ijebu zuwaOde, Mojoda zuwa Epe, da rukunin gidaje 527 da dai sauran su.
Somorin ya Kuma yi nuna da cewa, za a bi dukkannin Ka’idojin cutar COVID-19 za a yayin ziyarar ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.