Mutane biyu ne suka mutu a wani hatsarin da ya afku a mahadar Motoci na PZ da ke kan titin Benin zuwa Sapele a jihar Edo a karshen makon nan.
An ruwaito cewa hatsarin ya hada da wata mota kirar Toyota Bus da wata Babbar motar kirar Ford dake tsaye.
Wasu fusatattun matasa da suka yi dandazo a wurin da hatsarin ya afku nan take suka bankawa motar da ke dauke da abubuwan sha wuta.
Wani ganau ya ce direban bas din yana kan gudu sosai kuma ana cikin haka ne ya kutsa cikin wata babbar motar da ke tsaye, inda ya kashe mutane biyu nan take.
Ya ce hatsarin ya haifar da tsunkoson ababen hawa na tsawon sa’o’i da dama a kan babbar hanyar da ta saba cunkoso, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa sauya wasu hanyoyi na daban-daban.
Da aka tuntubi kwamandan sashin kiyaye hadurra na jihar Edo, Henry Benamaisia, ya tabbatar da afkuwar hatsarin tare da gargadin direbobin kan gudu, tuki mai hatsari, ajiye motoci ba bisa Ka’ida ba, da sauran nau’ukan sabawa dokar hanya.
BeBenamaisia ya baiwa masu ababen hawa tabbacin ci gaba da kokarin hukumar na rage hadurra a kan titin zuwa mafi karanci.
Sai dai ya shawarci jama’a da kada su dauki doka a hannunsu.
Sakon Edita: Anyi amfani da hoton dake samane domin a musalta lamarin