Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta amince da karin girma ga ma’aikata 772 na jami’ar Bayero malamai da wadanda suke a ɓangaren gudanarwa.
Mai magana da yawun Jami’ar, Lamara Garba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Kano, tare da aikowa da jaridar Dimokuraɗiyya.
Rikicin Shugabanci: Yan sanda sun Garkame majalisar dokokin jihar Filato
Zanga zangar adawa da zaben Iraqi ya rikiɗe zuwa Tarzoma
“Majalisar gudanarwar jami’ar ta amince da bukatar da mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu-Abbas ya gabatar, a wani bangare na ƙarin girma na shekarar 2021,” in ji Garba.
Ya ce an kara wa mutane bakwai karin girma zuwa matakin Farfesa, 18 na kusa da Farfesa (Associate Professors), yayin da 747 ma’aikatan da ba masu koyar ba, aka kara musu girma zuwa matsayi daban-daban.
“A cikin ma’aikata 747 da ba masu koyarwa ba, uku an kara musu matsayi zuwa matsayin mataimakin magatakarda.”
Ya ce karin girma na Farfesa da Mataimakin Farfesa ya fara aiki daga 1 ga Oktoba, 2020, yayin da na ma’aikatan da ba na ilimi ba daga 1 ga Oktoba, 2021.
Mai magana da yawun Jami’ar ya kara da cewa shugaban jami’ar ya bukaci sabbin ma’aikatan da aka kara musu girma da su tabbatar da karin girma da suka samu ta hanyar jajircewa da kuma nuna kwazo wajen gudanar da ayyukansu.