An nada Mista Jonny Baxter a matsayin mataimakin jakadan Burtaniya (DHC) a Legas dake Najeriya inda ya maye gurbin Ben Llewellyn-Jones, wanda kwanan nan ya kammala wa’adin shekaru uku a matsayin mataimakin jaka a Legas, Tribune Online ta rawaito.
Jonny ya kasance gogaggen jami’in diflomasiyya ne wanda ya yi aiki a sassa daban-daban na duniya.
KARANTA WANNAN: Tsaro: Gwamnan Kwara Ya Gabatar Da Motocin Sintiri Guda 32 da Babura 160
Kafin ya zama Mataimakin jakadan Burtaniya (DHC) a Legas, ya kasance jakadan Mai Martaba a Jamhuriyar Sudan ta Kudu daga watan Janairun shekarar 2021 zuwa Yuli 2023.
Sannan ya kasance Mataimakin Darakta, Sashen Kudi da Ayyuka a Ofishin Commonwealth da kuma ofishin cigaba na Waje – FCDO ( sai DFID) daga shekarar 2018 zuwa 2020.
Ya rike manyan mukamai daban-daban a Sashen Ci Gaban Duniya (DFID). Wadanda suka hada da gudanar da Sashen Ci gaban Bil Adama daga shekarar 2017 zuwa 2018, Babban Sakatare mai zaman kansa na Sakatariyar Gwamnati daga shekarar 2014 zuwa 2016.
Zakalika shugaban Sakatariyar Task Force daga shekarar 2013 zuwa 2014 duk a hedkwatar DFID dake London.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito Kafin waɗannan ayyukan Jonny ya yi aiki a kasashen Sudan, Iraq, Guyana da kuma Tanzania.
Don tunawa da isowarsa Jonny Baxter ya ce: “Na yi farin ciki da wannan sabuwar rawar kuma ina fatan yin aiki tare da mutanen wannan ƙasa mai girma, gami da waɗanda ke cikin gwamnati, a kamfanoni masu zaman kansu da kuma ƙungiyoyin farar hula, don yin duk abin da zan iya.
“Zan taimaka wajen gina Najeriya mai wadata da kuma karfafa dangantakar abokantaka da ke tsakanin jama’a da cibiyoyin kasashenmu biyu.”
A wani labarin kuma,Ba Zan Bada Kunya Ga Shugaba Tinubu da Majalisar Dattawa Ba – Keyamo
Mista Festus Keyamo, wanda aka nada a matsayin minista daga jihar Delta, a ranar Litinin ya ce ba zai bai wa Shugaba Bola Tinubu kunya ba saboda ya nada shi a matsayin minista.
Keyamo, wanda tsohon karamin minista ne a ma’aikatar samar da ayyuka yi da samar da albarkatu, ya kuma gode wa majalisar dattijai bisa wannan gagarumin la’akari da ta yi, yana mai cewa ba zai bai wa majalisar kunya ba.