Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara a ranar Litinin ya gabatar da sabbin motocin sintiri guda 32 da babura 160 don tallafawa zirga-zirgar jami’an tsaro a jihar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati za ta kara hada kai da masu ruwa da tsakai don inganta tsaro a yankunan karkara.
KARANTA WANNAN: Ba Zan Bada Kunya Ga Shugaba Tinubu da Majalisar Dattawa Ba – Keyamo
Gwamnan ya kuma bayar da motocin sintiri guda uku ga hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kwara (KWARTMA) domin inganta ayyukansu, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
“Yau wata rana ce a kokarinmu na karfafa tsaro a fadin jihar. Kowacce daga cikin kananan hukumomi 16 zata samun motoci biyu da babura 10 kowanne,” Gwamnan ya bayyana haka a wani takaitaccen taron da aka yi a gidan gwamnati da ke Ilorin.
“Mahukuntan kananan hukumomin su hada kai da duk masu ruwa da tsaki, ciki har da sarakunan gargajiya da ke yankunansu, sannan su tabbatar da cewa sun kulla alaka sosai da jami’an tsaro.
Hukumomin tsaro ba za su iya yin hakan su kadai ba. Suna buƙatar goyon bayanmu don tabbatar da cewa al’ummominmu suna cikin tsaro. Wannan shine dalilin da ya sa muke tabbatar da cewa suna da ingantaccen motsi don yin hakan. Muna rokonsu da su yi amfani da shi sosai”.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Rt. Hon. Yakubu Danladi-Salihu, ya yabawa gwamnan bisa wannan shiri, wanda ya ce zai taimaka wajen karfafa tsaro a kowane bangare na jihar.
“Tare da abin da muka gani a nan a yau, aikin cibiyoyin tsaro a fadin mazabu 24 sun sami sauki.Da wannan ne za a inganta tsaro sosai a dukkan kananan hukumomi 16.
“Wannan ya sake nuna cewa mai girma Gwamna yana nufin alheri ga jihar. Ya taka tasa rawar, kuma ina rokon masu rike da mukamai su yi amfani da shi yadda ya kamata. Hakan zai kawo cigaba mai kyau ga jihar,” inji shi.
Kungiyar Kananan Hukumomin Jihar Kwara (ALGON)/Shugaban Karamar Hukumar Ifelodun, Jide Ashonibare, ya yaba da rabon motocin, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen karfafa gine-ginen tsaro na kananan hukumomi a jihar.
“Muna godiya ga mai girma gwamna bisa wannan babban mataki. Za mu tabbatar an yi amfani da su yadda ya kamata domin karfafa tsaro a yankunan mu,” inji shi.
Babban jami’in hukumar KWARTMA, Akeem Adegboye ne ya karbi motocin a madadin hukumar, inda ya godewa gwamnan bisa wannan karimcin.
A wani labarin kuma, Cikakkun Jerin Sunayen da Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Wadanda Tinubu Ya Nada A Matsayin Ministoci
Majalisar dattawa a ranar Litinin ta tabbatar da mutane 45 a matsayin ministoci, kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya bukata.
DAILY POST ta rawaito cewa shugaban kasar ya aikewa majalisar dattijai jerin sunayen ministocin da aka nada a rukuni uku, wanda ya kunshi sunaye 48.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa majalisar dattijai ta tantance mutane 45 sannan ta tabbatar da su a ranar Litinin.