Jirgin farko da zai fara jigilar masu neman mafaka zuwa Rwanda zai tashi da mutanen ranar Talata, yayin da wadanda ba’a tashi da su ba, za su kasance cikin wasu jirage masu tashi anan kaba, kamar yadda Liz Truss ta bayyana.
Sakatariyar harkokin wajen na kasar ta ce zai “kafa ka’ida” tare da karya tsarin kasuwancin masu fataucin mutane zuwa burtaniya.
Baya ga haka, Firaminista Boris Johnson ya ce gwamnati ba za ta “janye ba ko jin kunya” kan sukar shirin nata.
Kafin tashin jirgin dai, Ana sa ran za a saurari karin wasu kararaki uku da mutanen suka shigar gaban wata, bayan da kotun daukaka kara ta yi watsi da yunkurin karshe na hana jirgin jigilar bakin hauren zuwa Kigali babban birnin kasar Rwanda da ke gabashin Afirka.
Ya zuwa yanzu, A ranar litinin mutane 138 ne suka isa Burtaniya cikin jiragen ruwa guda uku, tare da bakin haure sama da 10,000 da suka yi balaguron mai cike da hadari.
Anata jawabin da take magana da BBC Breakfast, Ms Truss ta tabbatar da cewa jirgin zai tashi kamar yadda aka tsara ko da kuwa mutane kalilan ne ke cikinsa, tana mai bayyana shi a matsayin “babban bangare na dabarun dakile muggan masu fasa-kwaurin mutane”.
Ms Truss ta kara da cewa gwamnati a shirye take ta fuskanci kalubalen shari’a a nan gaba kan tsare-tsarenta, ta kara da cewa, yana da matukar mahimmancj mutanen su sami kyakkyawar rayuwa a kasar su ta Rwanda.
Da aka tambayi Ms Truss a cikin shirin gidan rediyon BBC a yau ko jirgin zai tashi ko da ba kowa a cikinsa??, Ms Truss ta ce tana da yakinin cewa akwai mutane a cikin jirgin – amma ta kara da cewa ba ta za iya bayyana adadin yawan mutanen ba.
Ta kuma ki bayyana adadin kudin da gwamnatin kasar ta burtaniya zata kashe wajan amfani da jirgin da zaiyi jigilar bakin hauren, amma ta ce kudin da ake kashewa a safarar mutane da shige da fice ba bisa ka’ida ba na da matukar yawa.