Jagoran kungiyar matasan Arewa masu fafutukar neman kujerar Tinubu NYPT, Alh Abdullahi Tanko Yakasai, ya bayyana cewa Musulmi da Arewa ne kadai za a tsayar mataimakin dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sa jam’iyyar APC samun nassra, da gagarumin rinjaye a kan Jam’iyyar PDP wajen dawowa mulki a 2023.
Da yake bayyana hakan a tashar talabijin ta Arise a ranar Talata, Yakasai ya ce tikitin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a matsayin musulmi da musulmi zai yi kira ga jihohin arewacin kasar da galibinsu musulmi ne da su samu kuri’u domin samun nasara.
- KARANTA WANNAN LABARIN: APC ta kata yin asarar sanatoci 2 a hannun PDP
Jam’iyyun siyasa a kasar na da kasa da sa’o’i 72 su yi rajistar mataimakan su na shugaban kasa zuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, bayan kammala zabukan fitar da gwani a makon jiya.
Kuma an yi ta cece-kuce a kan yadda Tibubu yake musulmi zai zabi wanda zai yi takara Musulmi, inda wasu ke cewa Kirista ya nada tsohon Gwamna, wanda Musulmi ne.
Sai dai Yakasai ya yi imanin cewa abin da ya fi daukar hankali shi ne nasara ga jam’iyya mai mulki, inda ya nanata cewa Musulmi ne kadai zai iya tabbatar da hakan.
“Yawancin jihohin Arewa Ina tsammanin muna da uku wadan kiristoci suke kawai wadanda yawancinsu Kiristoci ne, jihohin Taraba, Benue da Filato. A cikin jahohin Arewa 19 mafi rinjaye Musulmi ne, me ya sa muke gujewa cewa jam’iyyarmu tana bukatar wadannan kuri’u.
“Muna bukatar tattara wadancan kuri’u domin samun shugabancin kasar nan a 2023 shi ne abu na daya.
“A duk lokacin da jam’iyyar za ta zabi wani, ta kan yi kokarin gabatar da wanda zai iya tattara kuri’u. Ina so ku fahimci wannan gaskiyar. Wani da zai iya ba mu wadannan kuri’u kuma mun samu gagarumin rinjaye,” inji shi.