Hukumar Shirya Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta sanar da ranar fara gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2023.
Wasan wanda zai gudana a Cote d’Ivoire, zai fara ne a ranar 23 ga watan yuni, zai kuma ƙare zuwa 23 ga watan juli.
KARANTA WANNAN LABARIN: Badaƙalar kuɗi: Kotu ta wanke Makusancin Buhari, Mohammed
Ƙasashe 24 za suyi gasar cin kofin, inda Hukumar CAF ta ɗauki matakin canja ranar gudanar da wasan AFCON daga Janairu zuwa Yuni, domin baiwa ƴan wasan damar su shirya.
Ƙasashen da suka samu nasara domin buga kofin za’a sanar dasu a ranar 21 ga watan Janairun Shekarar 2022.