Alamu sun nuna cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya umurci bankunan da su rika musayar kudaden kasashen waje ta kowace irin canjin kudi a cikin tagar Masu zuba jari da masu fitar da kaya bisa la’akari da yadda mai saye yake da shirye-shiryen masu sayarwa.
A martanin farashin canjin I&E ya tashi sosai zuwa Naira N610 kan kowacce dala, kamar yadda da karfe 12:50 na rana daga Naira N471.67 a daren jiya.
KARANTA WANNAN: CBN Ya Karyata Rage Darajar Naira
Duk da cewa har yanzu CBN din bai fitar da wata sanarwa ba, amma wasu shugabannin bankuna biyu sun tabbatar wa Vanguard cewa gaskiya ne CBN ya ba da umarnin ga bankunan.
Tasiri
A halin da ake ciki, wani ma’aikacin bankin zuba jari Comercio Partners, Nnamdi Nwizu, ya ce tasirin umarnin nan take yana kara habaka kudaden musaya na kasashen waje a cikin tattalin arziki da kuma kara hauhawar farashin kayayyaki yayin da farashin canjin I&E ya tashi matuka kamar yadda aka riga aka ambata kuma aka gani a yau.
A wani labarin kuma,Kano: Shirin Dawo Da Sarki Sanusi II Ba Gaskiya Ba Ne – Shugaban Masu Rinjaye
Majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana a matsayin wani hadadden labaran karya da aka rawaito na yunkurin yin gyara ga dokar majalisar masarautar jihar da nufin dawowar tsohon sarki Muhammadu Sanusi II.
Majalisar ta kuma bayyana rade-radin cewa za su tsige sabbin sarakunan Gaya, Bichi, Rano, Karaye guda biyar domin baiwa hambararren Sarki Muhammadu Sanusi II damar samun cikakken iko a matsayin Sarkin Kano da cewa ba gaskiya bane.
Kafofin sada zumunta sun yi ta zugwigwita labarin a ranar Larabar da ta gabata cewa Majalisar za ta sake duba batun masarautu, inda shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dala, zai karanta daftarin dokar 2023 a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni 2023.
An bayyana cewa an tsara majalisar za ta tattauna batun tare da amincewa da gyaran wanda daga baya zai bada damar tsige sarakuna da kuma dawo da Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, tare da amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba bayan kammala zaman majalisar, shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, ya bayyana labarin a matsayin labaran karya.
Hussaini ya ce babu wani yunkuri da zai sa ya karanta irin wannan gyara domin ba a taba tattauna batun ba.