Babban bankin Najeriya ya karyata ikirarin cewa ya karya darajar Naira.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin Daraktan Sadarwa na CBN, Isah AbdulMumin, ta ce an sayar da dala daya akan Naira N465 sabanin rahotanni,Punch ta rawaito.
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa wannan rahoton, wanda a tunanin jaridar ta kebanta, cike yake da karairayi da ruguza baragurbi, wanda ke nuna rashin sani ga kafafen yada labarai dangane da ayyukan ‘yan Najeriya a Kasuwar musayar kudin waje.
KARANTA WANNAN: NSCDC Ta Tura Jami’ai Don Farautar ‘Yan Bunburutu da Sanya Ido a Gidajen Mai
“Don kaucewa shakku, farashin canji a kasuwar (I&E), wanda aka sayar a safiyar yau (1 ga watan June 2023) dala daya tana akan Naira N465 kuma ya tsaya tsayin daka a kusa da wannan farashin na wani lokaci.”
Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Larabar da ta gabata ne CBN ya rage darajar Naira zuwa N630 akan dala $1 daga N461.6.
Hakazalika wani sako guda daya da hukumar ta CBN ta fitar a safiyar ranar Alhamis, ta ce “CBN bai rage darajar Naira ba.”
A wani labarin kuma,Zaben gwamna: Wasu ‘Yan Takarar Majalisa na PDP Sun Koma APC
Wasu ‘yan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Lokoja I da II Hon Ahmed Shehu Yabagi da Hon. Ishaiku Kashim Musa sun fice daga jam’iyyar sun koma APC.
APC ta bayyana jin dadinta game da matakin da ‘yan siyasar suka dauka na shiga jam’iyya mai mulki.
An bukaci masu sauya shekar dasu kara karfafa gwiwar magoya bayansu da su yi aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar.