Tun bayan tashi daga wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United da Brighton And Hove Albiol ake ta yin cece-kuce a dukkanin nahiyoyi guda bakwai da ake dasu a duniya dangane da wani abu da ya faru a wasan wanda hakan ba’a saba gani ya faru ba kokuma ace baya faruwa kwata-kwata, amma kuma a yau ya faru kuma ana ta ci gaba da yin cece-kuce kuma mauru’in daza ayi ta tattaunawa kenan a wannan makon.
Ayau dai an fafata wasan mako ba uku tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan guda biyu wasan da Manchester United tasha da kyar daci 3 da 2, wasan dai ɗan wasan Brighton ne ya fara jefa ƙwallon farko a daidai mintina na 40 yayin da Manchester United ta rama ƙwallonta ta hannun Dunk wanda yaci gidansu wato own goal a turance a dai dai mintina na 43.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Marcus Rashford ya sake jefa ƙwallo ta 2 a dai dai mintina na 55, haka zalika a dai dai mintina na 95 Brighton ta sake farke ƙwallon ta ta biyu inda March ya rama mata ƙwallon kenan, sai Bruno Fernandez ya sake jefa ƙwallo ta 3 a zare a mintina na 100 dai dai wadda itace ƙwallon da duniya take ta yin cece-kuce a kanta.
Abin da ya jawo cece-kucen shine wasan an busa tashi a 2 da 2 wato alƙalin wasa ya kawo ƙarshen wasan kenan, faman minti ɗaya na ƙarshe daya rage a tashi Manchester United ta sami abin da ake cewa bugun kusurwa wato corner kick inda bayan sun buga sai suka yiwa alƙalin wasa ƙorafin cewa ƙwallon ta gogi hannun ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brighton inda sai bayan an tashi a 2 da 2 alƙalin wasa ya je ya duba na’urar tantace kyawun ƙwallo sannan ya dawo ya bayar da bugun daga kai sai mai tsaron gida inda Bruno Fernandez ya jefa ƙwallo ta 3 a mintina na 100 dai dai.
An fafata wannan wasa a filin wasa na The American Express Community dake birnon Brighton a ƙasar ta Ingila kuma alƙalin wasan da ya jagoranci wannan wasa shine Chris Kavanagh wanda shine ya bayar da bugun daga kai sai mai tsaron gidan, sai dai abin da yasa ake ta yin cece-kuce shine ba a taɓa ganin hakan ta faru ba tunda aka fara yin amfani da ita kanta na’urar wato VAR.
Daman wannan na’ura wasu suna ta cewar kawai cutarsu ta keyi yayin da wasu suke cewar gyaramusu wasa ta keyi, sai dai na’urar ita kamar gireda take inji Hausawa wato idan ta tashi yin rusau to ta kan kowa ma bi ta keyi, sai dai wasu suna zargin kamar akwai ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suke shafaffu da mai ne inda na’urar bata fiye yin aiki a kansu ba inda wasu suke zargin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United tana cikinsu.
Idan akayi tariyar baya dai za a ga cewar koda a kakar wasan data gabata alƙalan wasa sun baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United bugun daga kai sai mai tsaron gida sau 23 inda mafi yawansu sai anje an duba wannan na’ura sannan ake basu wannan bugun na Fenarti wanda masana sukayi ta cece-kuce akan hakan.
Daga ƙarshe jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta tattauna da Abubakar akan wannan batu daya faru a yau wanda shima magoyin bayan Manchester United ne dake jahar Adamawa wato Arewa maso yammacin ƙasar Najeriya inda ya bayyana cewar:
“Eh jama’a suna ta cewa alƙalin wasa yayi ba dai dai ba kuma shi a wajensa yana ganin dai dai yayi, nima dai naga abin banbarakwai amma kuma tunda mu munyi nasara to koma me za ace sai dai ace tunda munsami maki 3”