Shugaban mulkin sojan kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan tawaye sama da 40, da nufin share fagen gudanar da tattaunawar kasa a karshen watan Agusta.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Doha bayan shafe watanni kasar Qatar na shiga tsakanin.
Amma babbar kungiyar ‘yan tawaye, Front for Change da Concord a Chadi ta ki sanya hannu kan wannan sabuwar yarjejeniyar.
Ta dage kan cewa Mista Déby ya ware kansa daga zaben da za’a gudanar a kasar.
An Shiga Zullumi A Abuja Yayin Da ‘Yan sanda Suka Yi Arangama Da Yan daba
Ya karbi ragamar shugabancin kasar ne a shekarar da ta gabata bayan mahaifinsa Idriss Deby ya rasu a lokacin da yake kan gaba wajen yakar ‘yan tawaye.
A wani labarin kuma.
Yanzu-Yanzu: An Saki Jushua Dariye Da Jolly Nyame Daga Gidan Yari
An sako tsoffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Sanata Joshua Dariye, da Jolly Nyame daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Wannan na zuwa ne watanni uku bayan afuwar da majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi a ranar 14 ga Afrilun shekarar 2022.
Wata majiya daga gidan gyaran hali ta shaida wa wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa an saki tsoffin gwamnonin ne da misalin karfe 2:15 na ranar yau Litinin.
Haka kuma an sake wasu fursunoni uku daga cibiyar gyaran hali na Suleja a jihar Neja.
“An yi musu afuwan ne bisa fama da rashin lafiya, tsofa, da kuma da’a da suka nuna yayin da su kike cikin cibiyar gyaran halin” inji shi.
Sai dai duk Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidan Rediyon Najeriya Abubakar Umar bai yiwu ba amma wani jami’in sashen ya ce yana cikin wani taro.
Nyame dai zai yi zaman gidan yari na shekaru 12 ne bisa samunsa da laifin karkatar da Naira biliyan 1.64 a lokacin da yake gwamnan Taraba, yayin da Dariye ke zaman gidan yari na shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan 1.126.
Matakin da majalisar zartaswa ta kasa ta dauka na sakin taofin gwamnonin biyu ya haifar da cece-kuce a fanin kasar nan.