Akalla kungiyoyi 12 ne suka yi nasarar samun gurbu a zagaye na 16 na gasar zakarun nahiyar Turai na wannan shekarar.
Daily Post ta ruwaito cewa, Wannan nazuwa ne bayan buga wasannin da aka fafata a jiya Laraba a Babban gasar Zakarun Nahiyar Turai a fadin kasashen.
KARABTA WANNAN LABARIN: Wata Mata Ta Dabawa Habibinta Kwalba A Wuya, Ya Mutu Har Lahira
Liverpool ta samu rabauta ne bayan doke Ajax da ci 3:0 da ta yi a gidan Ajax din. Yayin da itama Inter Milan ta shiga cikin jerin wadannan kungiyoyi da suka kai bantan su bayan Casa Viktoria Plezen da 4:0
FC Porto ma ta kai bantanta bayan ta yi nasara kan Club Brugge da ci 4:0
Kawo yanzu dai akwai guraben kungiyoyi hudu ne wanda kuma za’a samu cike gurbin nan ne kawai a ranar wasan karshen na rukunin.
Kawo yanzu kungiyoyin da suka haura zuwa zagaye na 16 a gasar na Champions League sun ne
Real Madrid
Manchester City
Napoli
Bayern
Club Brugge
Chelsea
PSG
Benfica
Dortmund
Inter Milan
Porto
Liverpool
Sai dai Bercelona, Sevilla, Da Atiletico Madrid dukkannin su sun yi kasa ne zuwa gasar Europa.
Bercelona ta sami koma bayan ne bayan ta sga kashi a gida a hannun kungiyar Kwallon kafa ta Bayern.
A WANI LABARIN KUMA: Buhari Ya Nemi Yan Korea Su Kara Zuba Jari A Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci manyan ‘yan kasuwan kasar Koriya da su kara zuba jari a Najeriya.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da wakilan kamfanoni da masana’antu na Koriya a gefen taron kolin na duniya na 2022 a babban birnin kasar Koriya ta Kudu, wato Seoul