Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea dai za a iya cewa tafi kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa cefane a kakar wasa ta bana duba da irin zaratan ‘yan wasan da ƙungiyar take saye kuma kusan kowannensu sai da aka kashe zunzurutun kuɗaɗe kafin a sayo shi daga ƙungiyar ƙwallon ƙafan da yake zuwa birnin London wato inda ita kanta ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Chelsea take kenan a ƙasar ta Ingila.
Sai dai akwai maganar da Hausawa ke cewa mai ruwan ido gama kasuwa da yawo idan anjima ka sayi dameji, kokuma suce an yi rashin sa’a an auro amaryar da bata iya girki ba amma kuma an kashemata kuɗi wajen yin cefane a kasuwa. Domin kuwa Chelsea ta yi siyayyar da za a iya cewa ya kamata duk wanda suka kama to su lallashi.
Sai dai daga fara fafata sabuwar kakar wasa ta bana ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Chelsea ta fara gamuwa da tasgaro na rashin nasara inda za a iya cewa a sabuwar kakar wasan gasar ajin Firimiya ta Ingila da aka fara inda aka buga waaannin mako na 3 har ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta rasa maki guda 5 wato tayi rashin nasara a hannun Liverpool sannan kuma ta buga 3 da 3 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Brom. Za a iya cewa kwata-kwata a wasan farko ta sami nasara wato wasan data doke Brighton daci 3 da 1.
Sannan gashi a wasan gasar League Cup na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta sami nasara a kanta daci 5 da 4 ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka tashi wasa kunnen doki da aka kwashe mintuna 90 wato 1 da 1. Sai dai za a iya cewa guda daga cikin ‘yan wasan Chelsea sababbi data sayo wato Timo Werner ne ya jefa ƙwallonsa ta farko a jiya a raga Tottenham.
Sai dai a ita wannan gasar ta League Cup za a iya cewa Chelsea naci gaba da kafa mummunan tarihi bayan da aka fitar da ita a wasan na jiya, amma kuma mummunan tarihin a ɓangaren bugun daga kai sai mai tsaron gida a ita kanta wannan gasa kenan.
Jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta binciko cewa a wasan na League Cup a dukkanin wasanni guda 8 da Chelsea ta buga a gasar harta kaisu ga bugun daga kai sai mai tsaron gida to tayi rashin nasara a wasanni guda 6, kawai a wasanni guda 2 tayi nasara. Sai dai wasannin guda uku duka a wasan zagaye na 4 ake fitar da Chelsea wato da wasan da suka fafata da Burnley a kakar wasa ta 2008 zuwa 2009 da wasan da suka fafata da Stoke City a kakar wasa ta 2015 zuwa 2016 da kuma wasan da suka fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham a daren jiya wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.
Sai dai wasu na ganin cewar kamar mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea wato Frank Lampard yana nuna ƙuruciya da kuma rashin sanin yadda zai sarrafa ‘yan wasan na Chelsea ganin cewar kusan kowacce lamba akwai mutane guda 3 da suke fafatawa a wajen amma kuma wajen yadda zai fito da ‘yan wasan ya sami nasara yana bashi matsala sosai da sosai.
Jiya dai ta tabbata cewar yaro da mai gidansa sun jagorancin ƙungiyoyin guda biyu wato Frank Lampard da mai gudansa Jose Mourinho ganin cewar a shekarun baya shi Mourinho ya horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea kuma lokacin Lampard yana a matsahin ɗanwsa kuma kusan duk wasu nasarori da ake nema Mourinho ya kawowa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a lokacin da yake horas dasu.
A ƙasar ta Ingila dai Mourinho ya horas da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ita kanta Chelsea da Manchester United yanzu kuma gashi yana horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham inda za a iya cewa dukkanin ƙungiyoyin na Chelsea da Tottenham a birnin London suke.