Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda.
DAILY POST ta rahoto cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan shine Alamatu Abiodun Mustapha.
KARANTA WANNAN: Najeriya Na Bukatar Sama Da Jami’o’i 500 Don Karbar Dalibai – Tsohon Shugaban NUC
Alamatu, yana cikin sabbin kwamishinonin ‘yan sanda takwas da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta nada.
A cewar wata sanarwa a ranar Juma’a da shugaban ‘yan jarida da hulda da jama’a Ikechukwu Ani,ya fitar yace “Hukumar ta amince da nadin tare da tura kwamishinonin ‘yan sanda takwas zuwa rundunonin jihohi.”
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Sabbin kwamishinonin ‘yan sandan jihohi da aka nada sune; Godwin Aghaulor, Jihar Borno; Adelesi E. Oluwarotimi, Jihar Kwara; Adebola Ayinde Hamzat, Jihar Oyo; Augustina Ogbodo, Jihar Ebonyi.
Sauran sune Samuel Titus Musa, Jihar Kebbi; Aderemi Olufemi Adeoye, Jihar Anambra;Stephen Olarewaju, Jihar Imo; da Alamatu Abiodun Mustapha, Jihar Ogun
A wani labarin kuma, NUJ Ta Caccaki ‘Yan Sanda Kan Yadda Suke Muzgunawa Wakilan Kungiyar
A ci gaba da taronta na watan Yuni da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida NUJ ta Ifeanyi Ugwuanyi dake Enugu, kungiyar ta caccaki ‘yan sanda kan cin zarafin ‘ya’yanta a yayin gudanar da ayyukansu.
A cikin sanarwar da sabon zababben sakataren kungiyar, Dame Ifeoma Amuta ya fitar,yace kungiyar ta NUJ ta yi nazari sosai kan al’amuran da suka shafi ‘yan kungiya, da kuma al’umma.
Sannan ta fitar da wasu kudurori, wadanda suka hada da bacin rai dangane da yadda ake ci gaba da rufe ’yan jarida a manyan abubuwan da ke faruwa a jihar.