Tsohon shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya bayyana cewa Najeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 220, na bukatar samar da jami’o’i sama da 500 domin biyan bukatun ‘yan kasa, Tribune Online t rahoto.
Rasheed ya yi watsi da jahilci ko barna da sukar da ake yi wa Gwamnatin Tarayya na amincewa da kara yawan jami’o’i.
KARANTA WANNAN: NUJ Ta Caccaki ‘Yan Sanda Kan Yadda Suke Muzgunawa Wakilan Kungiyar
Ya kara da cewa jami’o’i 261 da ake da su a kasar nan ba su isa ba, idan aka yi la’akari da yawan wadanda suke yin jarabawar shiga manyan makarantu UTME duk shekara.
Da yake jawabi a wani takaitaccen biki da aka yi a Abuja inda ya mika ragamar shugabancin hukumar ga mataimakin babban sakataren gudanarwa, Mista Chris Maiyaki, Rasheed ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din na sa.
Babban Sakatare, Mista Andrew David Adejo, ya umarce shi da ya mika ragamar mulki ga Mataimakin Babban Sakatareen Gudanarwa har sai an nada wani kwararren shugaba.
Rasheed ya fayyace cewa murabus din nasa wanda ya zo shekara biyu a wa’adinsa na biyu, ya biyo bayan wasu dalilai ne na kashin kansa da kuma burinsa na komawa Jami’ar Bayero Kano domin ci gaba da aikin koyarwa.
Ya bayyana cewa burinsa na rayuwa shi ne ya zama Emeritus farfesa, dalilin da ya sa ya yi fatan kammala aikinsa a jami’a, domin ba za a iya kiran mutum da Emeritus farfesa ba sai ya kai ga haka.
Shugabancin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) na ci gaba da adawa da abin da suka bayyana a matsayin yawaitar jami’o’i a Najeriya, musamman wadanda gwamnatocin jihohi suka kafa a fadin kasar.
Sai dai tsohon shugaban hukumar ta NUC ya jaddada cewa ilimi hakki ne na kowanne dan kasa ba wai kawai masu hali ba.
Ya yi imanin cewa, akwai bukatar a samar da karin jami’o’i don cike gibin da ake samu wajen karbar ‘yan takara, inda ya nuna cewa a halin yanzu kashi 1 cikin 100 na al’ummar kasar ne ke karatu a jami’o’in Najeriya.
Rasheed ya mika godiyarsa ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nada shi a shekarar 2016 tare da sake nada shi a karo na biyu.
Sannan ya kuma yi kira ga ma’aikatan Hukumar da su ba wa magajinsa goyon baya, domin ci gaba da inganta harkar koyo da koyarwa a tsarin jami’o’in Najeriya.
Mukaddashin shugaban hukumar, Mista Chris Maiyaki, ya yi alkawarin yin aiki tare da hukumomin hukumar don tabbatar da cewa wadanda suka kammala karatun jami’a za su yi gogayya da takwarorinsu na duniya.
A wani labarin kuma, Ban Yi Nadamar Gine-Gine da Na Rushe a Kano Ba – Abba Gida-Gida
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce bai yi nadama ko kadan ba a kan aikin rushewa da kwato dukiyoyin jama’a da gwamnatin da ta shude ta yi ba bisa ka’ida ba tare da raba wa shanu masu tsarki.
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da yake karbar bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero tare da hakimai da sauran ‘yan majalisar Masarautar suka kai wa Gwamnan ziyarar Sallah a gidan gwamnati a wani bangare na bukukuwan Sallah.