Matasan karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun ce, `yan bindiga da suka addabi garin sun kashe mutum 14 a hanyar Batsari zuwa Safana da ke jihar ranar Litinin, yayin da suka kashe mutum 19 a cikin makon nan duk a a cikin garin.
Matasan sun bukaci a sako wasu ‘yan banga da jami’an ‘yan sanda suka tsare saboda ya kashe wani dam bindiga a yankin. Matasan sun yi kiran ne a karkashin kungiyar matasan Batsari kuma sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin su game ci gaba da kisan gillar da ake yi a unguwanni da kauyukan garin.