Gwamnatin Zamfara ta ce mutum akalla dubu 2 da 619 ‘yan bindiga suka kashe sakamakon hare-haren da suka rika kaiwa sassan jihar.
Yayin taron manema labarai jiya Juma’a a garin Kaduna, kwamishinan yada labaran jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ya ce ‘yan bindigar sun salwantar da dubban rayukan ne a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2019.
Baya ga kuma mutane fiye da dubu biyun da suka kashe, Kwamishinan yace ‘yan bindigar sun sace wasu mutanen akalla dubu 1 da 190 da kuma dabbobi dubu 14 da 378 cikin shekaru 8.
Dosara ya kara da cewar kawo yanzu mutane sama da dubu 100 ne suka tsere daga muhallansu, sakmakon tashin hankalin ‘yan bindiga a sassan Zamfara, yayin da ita kuma gwamnatin Zamfara ta kashe naira miliyan 970 wajen biyan kudin fansar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Wani batu kuma da ya dauki hankula shi ne kokawar da gwamnatin Zamfarar ta yi kan adadin ‘yan bindigar dake addabar sassan arewacin Najeriya da ta ce ya kai dubu 30 a sansanoni fiye da 100 a jihar.
Sai dai gwamnatin ta ce shirinta na sulhu da ‘yan bindigar zai ci gaba da gudana, la’akari da muhimmancinsa wajen maido tsaro a jihar.