Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana cewar dukkanin magance wata matsala tana buƙatar ƙyamatar ta, tare da fito da masu cin hanci, domin wannan cutar Cancer ce a Ƙasar.
A cewar sa Shuwagabanni kaɗai waɗanda suke da son Cigaba, bawai samun riba ba, su zasu iya kawo Wannan gyara.
Osinbajo yayi wannan jawabin a ranar Juma’a a Abuja a taron farko na mabiya cocin katolika da taken “samun cigaba ta hanyar gaskiya da adalci, haɗin kai, da cigaban Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba rashin lafiya ta kai Tinubu Landan ba, yaje ne domin neman shawarwari — Cewar Mai Taimaka masa
Babban Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa akan Kafafen Yaɗa Labaru Laolu Akande ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya sanyawa hannu a daren Juma’a mai taken “Shuwagabanni kaɗai masu Son cigaba, ba samun riba ba, su zasu iya kawo gyara a Najeriya.
Mataimakin shugaban Kasar wanda ya bayyana cin hanci a matsayin cutar daji, yace Cancer a gwamnati a ko’ina itace cin hanci.
Ya ƙara dacewa, samun wani abu na cigaba dole ya ƙunshi “rashin gajiya wajen gaskiya da taka tsantsan ga masu riƙe da ofisoshi, dole mu ƙyamata, tare da magance cin hanci, da masu aikata shi.
Comments 1