- Shugaba Tinubu ya umurci NEC, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ta fara aiki babu kama hannun yaro.
- Hakan ya kawo karshen kashe zunzurutun kudin da Najeriya take bayarwa har kimanin Naira tiriliyan 4 a duk shekara wajen bayar da tallafin man Fetur.
- Yan kasuwan sun bada gudummawar motocin bas guda 100 don taimakawa nasarar shirin cire tallafin man Fetur.
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa, NEC, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ta fara aiki tare da sanya baki domin inganta tasirin cire tallafin fetur ga jama’a,Vanguard ta rawaito.
Umurnin shugaban kasar ya zo ne a ranar da gwamnonin jihohi 36 na tarayya suka kifar da ra’ayin gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur.
KARANTA WANNAN: Sojoji Sun Lalata Haramtacciyar Matatar Mai Da Injinan Masu Aikin
Hakan dai na zuwa ne yayin da a jiya manyan ‘yan kasuwar man fetur suka baiwa gwamnatin tarayya tallafin manyan motocin bas guda 100 da kudinsu ya kai zunzurutun kudi har Naira biliyan 10 domin dakile tasirin cire tallafin fetur.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ne ya bayyana haka bayan ya jagoranci wasu manyan ‘yan kasuwar man fetur a wata ziyarar ban girma da suka kai wa shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a jiya.
Da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin tarayya bayan kai ziyarar ban girma, gwamnan ya ce ’yan kasuwar sun je fadar shugaban kasa ne domin nuna goyon bayansu ga shugaban kasa kan matakin da ya dauka na kawo karshen biyan tallafin fetur.
Ya ce matakin na Tinubu ya nuna jajircewarsa wajen kawar da zubar jinin da ya addabi kasar nan tsawon shekaru da dama.
Ya ce kasar na kashe kimanin zunzurutun kudi Naira tiriliyan 4 a duk shekara wajen bayar da tallafi, wanda daga yanzu za a kai shi ga kwamitin raba asusun tarayya, FAAC, domin rabawa tsakanin gwamnatoci uku.
Gwamnan ya ce duk da cewa za a samu rashin jin dadi a bangaren jama’a, amma a karshe matakin zai yi tasiri domin kuwa ba za a samu riba ba, ba tare da jin zafi ba.
Dame Winifred Akpani, Shugabar DAPPMAN, ta ce sun kai ziyarar ne domin nuna goyon bayan manyan ‘yan kasuwar mai ga gwamnatin tarayya.
Ta ce suna sane da irin wahalhalun da cire tallafin ya haifar a kasar, inda ta bayyana fatansu na ganin zai sake mayar da kasar zuwa wani mataki.
Dame Akpani ta bayyana cewa Najeriya a watanni ukun farko na shekarar 2023, ta kashe sama da Naira tiriliyan 2, inda ta kara da cewa idan aka ci gaba da biyan kudin, adadin na iya haurawa zuwa Naira Tiriliyan 7 a karshen shekara.
Ta ce ta hanyar tallafin fetur Najeriya ta kasance tana ciyar da kasashen da ke makwabtaka da ita, inda ta ce ba za ta iya ba da tallafin man fetur ga kasashen Afirka ba, yayin da tattalin arzikinta ke ci gaba da zubewa.
‘Yan kasuwan sun bayyana aniyarsu ta ba da gudummawar motocin bas guda 50 zuwa 100 na jama’a don taimakawa nasarar shirin, tare da fatan sauran kungiyoyin kamfanoni masu ma’ana za su yi hakan.
Gwamnoni Sun Marawa Tinubu Baya Kan Cire Tallafin Man Fetur
A halin da ake ciki, a jiya gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na kawo karshen biyan tallafin man fetur a kasar nan da kuma wasu tsare-tsare na gwamnati tun farko.
Gwamnonin da ke karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, sun bayyana goyon bayansu a ganawar farko da shugaban ya yi da su a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shuwagabannin jahohin da suka tattauna a wajen taron, karkashin jagorancin shugaban kungiyar NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, sun bayyana farin cikin su da matakin cire tallafin da shugaban kasa ya yi, da kuma shugabancinsa na bai-daya da kuma na jihohi.
A wani labarin kuma,Babu wani shiri na haramta kungiyar ASUU a karkashin Gwamnatin Buhari – Ngige
Tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ya karyata kalaman da dan majalisar wakilai Aminu Goro ya yi na cewa akwai wani shiri na haramta kungiyar malaman jami’o’i a karkashin tsohuwar gwamnatin shugaban kasa. Muhammadu Buhari.
Ngige, wanda ya rike mukamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi a tsawon shekaru takwas na gwamnatin Buhari ya bayyana kalaman da Goro ya yi a matsayin tarin karya da kage.