Rahotanni sun ce Antonio Conte ya dhirya tsab domin ya zama kocin Man Utd nan gaba akadan, amma sai idan kulob din ta nuna masa son lashe gasar zakarun Turai, in ji Daily Mirror.
Da yake magana kan Super Sunday, Gary Neville ya bayyana dalilansa na hana daukar tsohon Kocin Chelsea da Juventus a gasar Premier da Serie A wato Conte Conte, wanda a halin yanzu Bai da kungiyar da yake jagoranta
“Ba za su kawo wani koci ba. Za su cigaba da aiki da Ole, kuma dole ne ya ci wani abu a kakar wasa ta bana, ”kamar yadda ya bayyana a Gidan Talbijin na Sky Sports.
“Jose shine mafi kyawun manaja a duniya kuma ba zai iya yi ba. A ra’ayina ba zan kawo Conte a United ba domin Bai dace da United ba.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Lokaci ya zo da sai dai mu zuba Ido~Shu’aibu Lilisc
“Zan iya yin kuskure amma ban tsammanin shi ne ya da ce da Kungiyar ba.” a cewar Gary Nevile
Sai dai Neville yayi wadannan kalaman ne kafin Liverpool ta Lallasa United a Old Traford da ci biyar da Nema.
Wanda ahalin yanzu Ole ke cikin wani Hani da ka iyasa United ta hakura da shi domin Nemo Wanda zai maye gurbin Kocin.