Cibiyar Kula da dakile Cututtuka ta Nigeria (NCDC) ta ce, mutane guda Biyu sun mutu sanadiyar cutar COVID-19.
Hukumar NCDC ta sanar da hakan ta shafin yanar gizonta da a ranar Juma’a wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu da cutar ya kai 2,742.
NCDC ta kuma bayyana cewa, an samu ƙarin kamuwa da cutar guda 290 a cikin jihohi 14 da har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar ta NCDC ta bayyana cewa, Abuja ce ta daya a inda mutane 127 suka kamu, Legas na biye da 45, yayin da Kaduna a Arewa maso Yammaci ke matsayi na uku a rahotan na NCDC da mutane 28.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Cafke Mutane 15 da ake zargi da Satar Kayayakin Jirgin Kasa a Benue
Yayin da jihohin Kudu-maso-Kudu na Delta na da 18, Ribas 10, Edo 3 da Akwa Ibom ma nada 3, yayin da jihohin Arewa ta Tsakiya da suka hadar da Kwara, Filato da Nasarawa sun samu mutane 17, 13 da kuma hudu kowanne su.
Kazalika Hukumar ta kara da cewa, Zamfara ta samu mutane 10; Imo ta na da shida, yayin da Ekiti, Ondo da Oyo suke da biyar, uku da kuma daya, ko wanne su.
Hukumar ta kuma ce, karin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Nigeria sun kai adadin 207,210.
A karshe Hukumar NCDC ta shawarci ‘yan Nigeria da su dauki matakan kariya saboda duk nau’ikan bambance-bambancen COVID-19 guda huɗu suna yaduwa a cikin Nahiyar Afirka