Cibiyar dakile yaduwar Cututtuka ta Nigeria NCDC ta bayyana cewa, an Sami sabbin wadanda suka ka u da cutar Corona 78 a fadin Nigeria.
Cibiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da tafitar kan COVID-19 a jiya Lahadi.
A cewar rahoton NCDC, an samu masu cutar guda 78 a jihohi 11 dake fadin kasar nan, Wanda suka hada da: Legas (22), Kaduna (12), FCT (10), Benue (9), Imo (8), Akwa-Ibom (4), Delta (4) , Kano (4), Jigawa (3), Filato (1), Rivers (1).
Wannan yanzu ya kawo adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar zuwa 207,694.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar FRSC ta ja hankalin Matafiya kan hanyar Kogi
Daga cikin jimlar wadanda suka kamu da cutar, mutane 195,274 sun warke, yayin da 2,747 suka mutu har lahira, sakamakon kamuwa da cutar