Dan wasan JUventus, Cristiano Ronaldo ya zura kwallo uku ringis a ragar Cagilari a wasan gasar Seria A da aka buga a jiya Lahadi.
Wasan dai an tashi 3 da 1 ne. Wanda zura kwallon nan da Ronaldo ya yi ya sanya Daraktan kungiyar ta Serie A, Fabio Paratici ya ce dan wasan ne makomar Juventus.
Bayan tashi wasan Ronaldo ya taya kansa murna a shafinsa na Instagram, inda ya ce; ya ci kwallo 770 a duniyar kwallon kafa, wanda hakan ya sanya shi karya tarihin cin kwallaye da dan wasan Brazil, Pele ya yi a duniya.
Ronaldo ya ce yana cike da farin ciki bisa hakan, kuma yana da kwarin guiwa cewa zai ci gaba da karya tarihi a duniya, domin har yanzu yana da kwanji da karsashin buga kwallo. Sannan ya ce ba zai karaya ba, domin yana da kwarin guiwar cewa zai ci wa Juventus da kasarsa ta Portugal kofuna.
Wannan dai shi ne karo na farko da Ronaldo ya zura kwallo uku ringis a gasar Seria A ta kasar Italiya.