By Ishaq Dabai
Hukumar kula da cutuka masu ya duwa NCDC, ta sanar da adadin wadanda suka kamu da cutar a mai da gudawa inda mutane da suka kamu suka kai 65,145 sannan kuma tayi sana diyyar mutuwar mutane 2,141, a wuraren kula da marasa lafiya na CFR na kaso 3.3 daga jihohi 23 ciki harda birnin tarayya FCT a ranar 2 gawatan Satumba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa NCDC ta wallafa a shafin hukumar na cutuka masu ya duwa a ranar litinin.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN yace kasho 62 ya ragu na daga cikin wadanda suka kamu a cikin wannan satin da 33 (2,127) idan akayi la’akari da 3,098 na wadanda suka kamu a cikin sati 32.
A cewar binciken jihar Bauchi tana da masu cutar guda 855,sai jihar Katsina 396, sai jihar kano 306 inda a dadin su yakai kaso 73.2 na mutane 2,127 na wadanda suka kamu a cikin sati 34.
Sauran jihohi sun hadar da jihar Yobe tana da masu cutar guda 162,sai Zamfara 80,sai Neja 78,sai Borno 67,sai Sakkwato 45,sai Kaduna 41,sai Gombe 21,sai birnin tarayya Abuja FCT 18,sai Kebbi 17,sai Adamawa 15,Taraba 13,Nasarawa 10,Plateau 2 da kuma jihar Jigawa 1″,
Ita dai wannan cuta ta amai da gudawa tafara ne a cikin shekarar da muke ciki inda take kama yara ‘yan shekara 5 zuwa 14 a matsayin wadanda tafi kamawa a tsakanin maza da mata.
A gabaki daya wadanda suka kamu da cutar idan a kayi la’akari da kaso 51 mazane inda kuma kaso 49 matane.
Rahoton ya bayyana cewa jihohin da suke da masu cutar a mai da gudawa guda 23 ne ciki harda birnin tarayya Abuja FCT, sai Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, Kano, Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Nasarawa, Neja, Jigawa, Yobe, Kwara, Adamawa, Enugu, Katsina, Borno, Taraba, da kuma Birnin tarayya FCT.
A cewar rahoton na sati, jihohi 16 ciki harda FCT an samu 2,127, inji NCDC.
A cikin jihohi wadanda aka samu suna dauke da ita bayan gwajin da aka yiwa musu cutar na RDT a wurare guda 32 an tabbatar da ita a kwai Adamawa 11,Katsina 8,Kaduna 7,Borno 4,Taraba 1,Da kuma Yobe 1.
Hukumar kula da lafiyar jama’a ta kara da cewa cutar ta kashe mutane 48 a jihohi daban daban Bauchi 10, kano 7,Katsina 6,Taraba 5,Zamfara 4,Sokoto 4,Borno 4,Neja 3,Nasarawa 2,Kebbi 1,Yobe 1,kaduna 1.
Zubar da shara barkatai da rashin tsaftar ruwan sha yana bude kofar kamuwa da cutar, da rashin wanke hannu yayin cin abinci.