Ƙididdiga daga hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya NCDC ta nuna cewa a ranar Juma’a, an samu ƙarin mutum 1,544 da suka kamu da cutar korona a ƙasar.
A cewar bayanin da NCDC ta wallafa a shafinta na Tuwita, cikin sa’a 24 da ta gabata, mutum 12 ne cutar ta yi ajalinsu sannan mutum 411 sun warke har an sallame su daga asibiti.
Har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba da mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana ɗayan inda take da mutum 739 sai kuma jihar Plateau da ke biye da ita da mutum 168.
Ita kuwa Abuja babban birnin kasar na da mutum 153 da suka kamu da cutar sai kuma jihar Oyo-91, Nasarawa-90, Rivers-80, Kaduna-35, Edo-33 , Kano-29 da jihar Ogun-21.
Jihohin da ke da kasa da mutum 20 su ne Delta-19 da Sokoto-16 da Akwa Ibom-11 da Ebonyi-11 da Enugu-10 da kuma Osun-10.
Sauran masu kasa mutum 10 su ne Niger-9, Bauchi-8, Kebbi-8, Katsina-2 da kuma Taraba-1.
A Najeriya dai, gaba ɗaya mutanen da suka kamu da korona ya zuwa ranar Juma’a ɗin, sun kai 97,478 sannan an sallami mutum 78,552 daga asibiti bayan an tabbatar sun warke daga cutar kuma mutum 1,342 ne suka mutu tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.