Gwamnonin Nijeriya daga jihohi 36 a fadin kasarnan sun amince a yi musu allurar rigakafin annobar cutar korona kai tsaya ta gidajen Talabijin domin gamsar da al’ummar kasar kan ingancin allurar.
Dr Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriyar, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a Abuja, a yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridar fadar gwamnatin shugaban kasa jim kadan da kammala zaman sirri tsakaninsu da shugaba Muhammadu Buhari.
“mu ma muna son mu gamsar da al’ummarmu cewa mun yarda allurar tana aiki”. Ya tab batar.
Ya kara da cewa; idan aka yi duba da allurar foliyo da aka yi a kasar, hakan ya kara musu fahimta. Ya ce sun yi aiki da Hukumar lura da lafiya a matakin farko, PHDA, da kuma ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya.
“zamu ji dadi mu yi aiki da NCDC, Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasa, da kuma kwamitin shugaban kasa kan dakile korona, PTF, da kuma PHDA”, inji Kayode.
“a don haka zamu zama madubi a dukkanin jihohi”, ya tabbatar.