Kungiyar Amnesty International ta zargi manyan kasashen duniya da gazawa wajen hadin kai domin shawo kan annobar Korona sakamakon yadda su ke ci gaba da boye rigakafin cutar wanda har yanzu ya kasa kai wa ga wasu kasashe matalauta.
Rahotan shekara-shekara na kungiyar ya ce annobar korona ta bankado rashin hadin kan da ke tsakanin kasashen duniya, yayin da ta zargi Chana da wasu kasashe da ke amfani da annobar korona wajen take hakkin bil Adama.
Sakatare Janar na Kungiyar Agnes Callamard wadda ta yi mummunar suka kan yadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fitar da kasar daga Hukumar lafiya ta ce matakan da kasashe masu arziki ke dauka na babakere kan maganin rigakafin ya sanya kananan kasashe shiga tasku wajen tinkarar annobar.
Korona dai na ci gaba da haddasa asarar dimbin rayuka a sassan duniya, inda a baya-bayan an cikin kasashen Matalauta Kamaru ke matsayin kan gaba a jerin wadanda cutar ke tsananta.
Sai dai kuma a Nijeriya, cutar na kara raguwa, inda ake samun karancin mutanen da ke dauke da cutar. Sannan kuma an kwashe fiye da mako daya ba tare da cutar ta kashe wani a Nijeriya ba.