By Abbas Yakubu Yaura
Sabbin masu rajista a ci gaba da rijistar masu kada kuri’a a fadin Najeriya (CVR) sun kai sama da miliyan 8,855,996 kamar yadda aka fitar a ranar 2 ga watan Mayu.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce ta bada wannan bayanin a ranar Alhamis.
Ekiti: Kotu Ta Yankewa Yarima Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Kashe Wani Basaraken Gargajiya
Cikakkun labaran na kwata hudu, mako na uku ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 5,415,619 ne suka kammala yin rajista.
Jimillar mutane miliyan 2,379,063 ne suka yi rajista ta yanar gizo, yayin da miliyan 3,036,556 suka yi rajistar a ofisohi.
Wadanda suka kammala nasu sun hada da nakasassu dubu 45,412 (PWDs) da kuma matasa su kimanin miliyan 3,745,129.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta karbi aikace-aikace miliyan 15,789,718 domin sauya shekar masu kada kuri’a, da sauya katin zabe na dindindin (PVCs) da kuma sauya bayanan masu kada kuri’a.
A kididdigar da aka gudanar kimanin mliyan 8,330,813 maza ne, yayin da miliyan 7,458,905 mata ne.
Comments 2