Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta cire sunayen dukkan ‘yan takarar jam’iyyar Action Alliance (AA), ciki har da dan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), wanda Kenneth Udeze ya mika mata.
Umurnin, wanda aka bai wa manema labarai a Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata, ya yanke hukuncin cewa hukumar zaben ta bayyana sunayen ‘yan takarar da shugabannin jam’iyyar suka mika mata a karkashin shugabancin Adekunle Rufa’i Omoaje.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Umurci CBN Da Ya Saka Obasanjo Akan Takardun Kudin Naira Da Ake Shirin Sakewa Fasali
Kotun da ke karkashin mai shari’a Z.B Abubakar ta kuma ce hukumar zaben ta yi kuskure ne ta hanyar kasa ba da sunayen ‘yan takarar da bangaren Omoaje ya mika mata.
Omoaje a madadinsa da kungiyar Action Alliance ya tuntubi kotu domin neman hakkinsa kan rashin amincewa da ‘yan takarar da ya mika wa INEC a madadin jam’iyyar.
A hukuncin da kotun ta yanke, ana sa ran za a maye gurbin ’yan takarar da INEC ta riga ta bayyana ciki har da dan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-mustapha (mai ritaya) da jerin sunayen ‘yan takarar da Omoaje ya mika.
INEC ta bayyana Al-Mustapha a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA kuma tuni aka buga sunansa a shafin yanar gizon hukumar zaben.
Sai dai kuma da sabon hukuncin kotu,ana iya sanyawa a maye gurbin Al-Mustapha da wani wanda shugabancin Omoaje ya amince da shi.
Rahotannin kafafen yada labarai na cewa Al-Mustapha na iya fuskantar hadarin rasa tikitin takarar shugaban kasa na AA sakamakon karar da aka shigar akan sa.
Mai shari’a Abubakar wanda ya bayar da misali da sashe na 29 (1) na dokar zabe, 2022, ya bayar da umarnin cewa, INEC ta gaggauta fitar da sunaye da adireshi na dukkan ‘yan takarar da Omoaje ya mika a madadin kungiyar Action Alliance.
“Ta hanyar tanadin sashe na 29 (1) na dokar zabe, 2022, ya kamata INEC ta buga ta hanyar nunawa a ofishin da ya dace na INEC da kuma a shafinta na yanar gizo.”
Da yake mayar da martani game da ci gaban, Shugaban jam’iyyar AA na kasa, Adekunle Omoaje, ya ce Kenneth Udeze wanda ke nuna kansa a jam’iyyar an kore shi daga jam’iyyar tun ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2020 a yayin babban taron jam’iyyar na kasa a Osogbo.
A wani labarin kuma, Hukumar FRSC Ta Yi Gargadi Game Da Amfani Da Wasu Nau’ikan Motocin Lexus
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta gargadi ‘yan Najeriya game da amfani da wasu motocin Toyota Lexus kan “wasu manyan matsaloli da suke dauke dasu”.
Sanarwar ta fito ne a wata sanarwa da jami’in kula da ilimin jama’a na FRSC Bisi Kazeem ya fitar a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba.
Hukumar ta ce gargadin ya zama dole ne bayan da Kamfanin kera motoci na Toyota’s ya sake kiran da amayar da wasu motocin Lexus sama da dubu 14,799 “marasa kyau”.