Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta cafke wasu mutane shida da ake zargin sun yi wa wata mata tsirar tare da yin holinta a garin Agunese da ke yankin Afam-Mmaku a karamar hukumar Awgu ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba, 2022, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Kori Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam’iyyar AA
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wasu matasan al’ummar yankin da yawansu ya haura ashirin suka yi wa matar tsirara tare da yin holinta a ranar 27 ga watan Oktoba, 2022, bisa zargin cewa ta wulakanta wurin ibadarsu ta hanyar tsinke dodon gori a cikinsa.
“Saboda haka, an kama wasu maza shida (6) da ake zargi, ciki har da wani Okoro Stan mai shekaru 46, wanda ake zargin shi ne ya jagoranci wasu wajen aikata laifin duka tare da gabatar da wanda abin ya shafa a zagayen al’umma. Sauran sun hada da: Jonathan Nwangene mai shekaru 43, Maduabuchi Madueke mai shekaru 34, Obioma Nwangene mai shekaru 39, Anikene Samuel mai shekaru 24 da kuma Chukwuebuka Agu mai shekaru 32.”
“Bugu da kari, ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don kama wasu baki dayan su dake da hannu a cikin lamarin,” in ji sanarwar.
“A halin da ake ciki, binciken da ake yi kan lamarin ya nuna cewa wadanda ake zargin sun kuma yi wa mijin da kuma dan’uwan wanda abin ya shafa dukan tashi kisha manda tare da raunata jikinsu, a lokacin da suka yi yunkurin hana su aikata wannan aika-aika.
“Don haka, kwamishinan, yayin da yake yin Allah wadai da wadannan kalamai na cin zarafi, wulakancin da aka yi wa wanda aka azabtar, wanda ya saba wa wasu dokoki, musamman wadanda suka shafi mutuncinta da hakkin dan Adam, ya kara da cewa a gudanar da bincike cikin mafi kankanin lokaci kuma an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.”
“Don haka CP ya bukaci ‘yan jihar musamman masu rike da sarautun gargajiya da sauran shugabannin al’umma da su tabbatar da yin taka-tsan-tsan wajen aiwatar da ka’idojin gargajiya ko na al’ada a kan al’amuransu, musamman idan yin hakan zai haifar da saba wa dokar da kundin tsarin mulki ya tanada. muhimman hakkokin mutum.”
A wani labarin kuma, Atiku Ya Umurci CBN Da Ya Saka Obasanjo Akan Takardun Kudin Naira Da Ake Shirin Sakewa Fasali
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya kamata tsohon ubangidansa kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kasance a jikin takardar kudi da ake kudirin sake fasali domin zaburar da al’ummar Nijeriya gaba.
Atiku ya bayyana haka ne a ranar Asabar, 5 ga watan Nuwamba, 2022.
Abubakar ya kuma ce Obasanjo ya cancanci ya lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel saboda kwazonsa na shugabanci.