Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Manir Muhammad Dan Iya, ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Dan Iya ya sanar da murabus ɗin sa a wata takarda da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓar Kware, cikin ƙaramar hukumar Kware ta jihar Sokoto. Rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Duk da bani bace zaɓin mijina, ya aureni saboda ban tatse masa aljihu -Matar aure
Takardar na cewa:
“Na rubuto wannan takardar ne domin na sanar dake na daina zama mamba a jam’iyyar PDP tun daga ranar 8 ga watan Fabrairun 2023.
“Nagode da damarmakin da aka bani, waɗanda suka sanya na riƙe muƙamai da dama a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.”
Wannan ba ƙaramin koma baya bane ga jam’iyyar PDP, domin ficewar sa tazo ana saura kwanaki 16 a fara zaben shugaban ƙasa wanda za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, shine babban darektan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen.
Duk da cewa Dan Iya bai sanar da inda zai tattara ƴan kayansa ya koma ba, wasu majiyoyi sun bayyana cewa yana dab da komawa jam’iyyar APC.
Da Kun Zaɓe Ni Zaman Lafiya Zai Dawo -Atiku Abubakar Yasha Alwashi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya tabbatarwa da mutanen jihar Yobe zai dawo da zaman lafiya a jihar idan aka zaɓe shi.
Atiku ya kuma yi alƙwarin buɗe iyakokin dake tsakanin Nijar da Yobe domin samar da hanyar wucewar mutane da kayan amfanin gona.