Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.
Zaben dai ya gudana ne tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu, APC da kuma PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: INEC Ta Bayyana Sule A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Nasarawa
Jami’in da ke kula da tattara sakamakon zaben jihar Farfesa Yusuf Sa’idu na Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato ne ya bayyana hakan a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke hedikwatar INEC a Birnin Kebbi.
Ya ce an soke zaben wasu rumfunar zabe a kananan hukumomi 20 cikin 21 dake Jihar ta Kebbi.
Sa’idu ya ce: “Mun tara jimlar adadin PVC da aka tattara a rumfunan zabe kuma ya kai 91,829.
“Kuma a lokacin da muka duba sakamakon zaben, jam’iyyun siyasa biyu da suka jagoranci wannan takara, APC da PDP sun samu kuri’u 388,258 da 342,980 bi da bi. Idan muka kalli bambancin dake tsakani, ya kai 45,278.”
Ya yi nuni da cewa ba su da wani zabi illa duba dokokin zabe a shafi na 31 na dokar zabe ta 2022, sashe na 51 karamin sashe na biyu da na uku domin neman jagora.
A cewarsa, dokar ta kara da cewa, “Idan yawan kuri’un da aka kada a zabe a kowace rumfar zabe ya zarce adadin wadanda aka amince da su a wannan rumbun zabe, shugaban hukumar zai soke sakamakon zaben a wannan rumfar.
“Karamin sashe na uku na sashe na 51 ya kuma bayyana cewa inda aka soke sakamakon zabe kamar yadda karamin sashe na biyu ya tanada, ba za a sanar da zaben ba har sai an sake gudanar da zabe a yankin da abin ya shafa.
“Saboda wadannan tanade-tanade da kuma ikon da aka bani a matsayina na jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kebbi a shekarar 2023, ni Farfesa Yusuf Sa’idu na Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, na bayyana zaben gwamna a jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.”NAN
A wani labarin kuma, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Lashe Zabe A Kananan Hukumomi 12 Cikin 18 A Jihar Kudu
Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Cross River, Bassey Otu, ya lashe zaben kananan hukumomi 12 daga cikin 15 izuwa yanzu da jami’an tattara sakamakon zaben kananan hukumomi suka bayyana a daren jiya.
Ya doke abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Sandy Onor, wanda ya yi nasara a kananan hukumomi uku.