Ƴan Bindiga sun sako Mutane 36 da suka kama a Katsina, bayan shafe wata 1
Mutane 35 da Ƴan bindiga suka sace a Garin Guga dake Ƙaramar Hukumar Bakori, sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe wata guda a hannun su.
A cewar Alhaji Mahdi Danbinta Guga, Wanda Matar shi da Ɗiyar sa na daga cikin wanda ƴan bindiga suka sace, yace an sako su ne bayan sun biya kudi Naira Miliyan 21,000,000 da Al’ummar Guga Suka haɗa.
A yau suka sako su da Misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari ya Jajantawa Keyamo kan rasuwar Mahaifin sa
A Wani Labarin kuma
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya Mika Ta’aziyyar sa ga Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi Festus Keyamo SAN kan mutuwar Mahaifin sa.
Ta’aziyyar Buhari na ƙunshi a cikin wata sanarwa da Babban Mai Taimaka Masa akan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi.
Shugaba Buhari yayi ta’aziyya ga iyalan Keyamo, Abokai da Al’ummar Effurun dake Karamar Hukumar Uvwie ta Jahar Delta a makoki sa, wanda ya kasance Shugaba mai daraja, mai Son ɗiyan sa,da ya koyar dasu yanda zasu yi Shugabanci.
A matsayin na Uba dake girmama kowa, ba tare da nuna bambancin wani abu ba, Shugaban Ƙasa ya yi amanna cewa Pa Keyamo ya kasnace Mai son Cigaban Najeriya, inda ya shafe rayuwar sa a Kaduna da Ilaro ta Jahar Ogun, kafin komawa Ughelli.
Shugaban Ƙasa yayi kira ga iyalan Keyamo dasu yi koyi da kyawawan ɗabi’un sa a matsayin sa na Uba kuma Kaka.