Ƴan Fashi da makami a ranar Talata da rana, sun sake kai farmaki a bankin Wema dake Iragbiji dake0 ƙaramar hukumar Boripe ta Jahar Osun.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton da misalin ƙarfe 3:33 na rana, ƴan fashi da makamin suna cikin bankin, ƴan mitoci kaɗan daga fadar Aragbiji ta Iragbiji.
Mai Magana da Yawun Rundunar Jami’an tsaron farin kai Daniel Adigun ya tabbatar da faruwar lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Ana Fargaban Mutane da dama sun Mutu, yayin da wani Wurin Hakar Ma’adanai ya rufta a Benue
Ya bayyana cewa, har yanzu babu cikakken bayanai akan yadda lamarin ya faru.
Wannan harin na zuwa ne, wata ɗaya bayan ƴan fashi da makamin sun farmaki bankuna guda biyu a Iree jahar Osun, wanda ya haifar da tsoro a zukatan masu ziyartar bankin.