Da Ɗuminsa: An Ekweremadu, Matar sa kan yunkurin canja wa Ɗan su Halitta a Landan
Ike Ekweremadu Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai na Ƙasa, da Matar sa Beatrice, an kama su a Ƙasar London.
A cewar Ƴan Sanda, an kama su ne da laifin taho da yaro zuwa Landan domin canja mashi halittar Jiki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Amotekun ta kama mutanen da ake zargi da kitsa harin ta’addancin Cocin Owo
Yaron wanda ba’a sanar da sunan sa, a halin yanzu yana wajen ƴan sanda, a yayin da Sanatan da Matar shi suke tsare a magarƙama na tsawon awanni, kafin kai shi Kotun Majistare na Uxbridge.
A cikin wata sanarwa, Ƴan sanda sun ce “mata da miji an kama su da laifin taho wa da yaro zuwa Landan domin cire wasu sassan jiki.
“Tuhume tuhumen ya biyo bayan bincike da ƴan Sanda suka yi ɓangaren manyan laifuka.
“Ike Ekweremadu ɗan Najeriya an kama shi da laifin ɗauko wani yaro da ba nashi ba, domin cire mashi wasu sassan jiki.