Da Ɗuminsa: APC ta tabbatar da Lalong a matsayin DG na yakin neman zaben Tinubu
A ranar Alhamis din da ta gabata ne jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da Gwamnan Jihar Filato kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong a matsayin Babban Darakta na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa.
Shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan ga Manema Labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari, a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jahar Plateau Ta Ƙwace Lasisin Duk Makarantun Firamare, Sakandare masu zaman kansu
Ya ce, “Mun zo nan ne domin ganin shugaban kasa da yi masa bayani da kuma samun amincewarsa kan tsare-tsaren da muke yi dangane da yaƙin neman zabe.
“Kuma da zarar mun sami yardarsa, zamu yi bayani. Muna tare da Shugaban kasa da kuma daidaikun mutanen da za su taka rawa daban-daban a yakin neman zabe.
“DG na kamfen yana zaune a dama na a nan. Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato.
“Mai magana da yawun shine Festus Keyamo. Mataimakiyar kakakin ita ce Hannatu Musawa Wannan shi ne abin da muka zo don tattaunawa da shugaban kasa.”
Adamu ya bayyana cewa zaben Lalong ya ta’allaka ne kan yadda ya iya yin ayyukan da ake bukata domin tabbatar da nasarar tikitin Tinubu-Shettima a zaben shugaban kasa na badi.
“Yana da ikon yin hakan. Shugabancin jam’iyyar ya ga cewa yana iya tafiyar da harkokin kamfen din,” in ji shi